loading-texture
MURYOYIN DA BA A SAURARA BA
Waɗannan labarai na ɗauke ne da cikakkn bayani game da musgunawa da tashin hankali da cin zarafin da ya shafi sad
Domin kara fahimtar matsalar, sai kukunna sauti.
0

Maharan Boko Haram sun ɗauke ni a matsayin fursunan yaƙi. A lokacin ina ‘yar 14. Kwanaki uku bayan mun isa jeji na yi ƙoƙarinin gudu, amma aka sake kama ni. An yi mini horo sakamakon hakan. An sanya mu cikin bukka tare da wasu yara da suka yi ƙoƙarin su ma su gudu.

https://www.unfpa.org/ha/unheardvoices/Aishatu
Danna ka saurara

Maharan Boko Haram sun ɗauke ni a matsayin fursunan yaƙi. A lokacin ina ‘yar 14. Kwanaki uku bayan mun isa jeji na yi ƙoƙarinin gudu, amma aka sake kama ni. An yi mini horo sakamakon hakan. An sanya mu cikin bukka tare da wasu yara da suka yi ƙoƙarin su ma su gudu.

Abincinmu a kullum ya kasance bulala 20 da safe sannan 10 da yamma.

Na samu damar tserawa a yayin da ɗana yake da wata bakwai. Na samu haɗuwa da ‘yar uwata wadda ita ma aka kamata, daga baya ta samu damar tserewa. A karshe, Allah ya sa muka haɗu da mahaifiyata. Na ga tsananin tashin hankali. Yayin da na rufe idanuna sai in rinƙa tunawa da baya, sannan sai in ji tamkar ina a Sambisa ne. Yanzu ina jin dama-dama, ina cikin nishadi, ina da abokanai kuma ina iya cin abinci, sannan kodayaushe ina jin son in fita waje.

story-letter
*An canza sunan domin matsalar tsaro

Hatta da wadanda suka samu kubuta daga masu cin zarafinsu, tunanin abinda ya faru yana nan biye da su cikin tunanin daruruwan mata, kusan duk tsawon rayuwarsu.

A TSAWATA. A DAINA CIN ZARAFIN JINSI
WANDA YA ƊAUKI HOTUNA SHI NE: Etinosa Yvonne