loading-texture
MURYOYIN DA BA A SAURARA BA
Waɗannan labarai na ɗauke ne da cikakkn bayani game da musgunawa da tashin hankali da cin zarafin da ya shafi sad
Domin kara fahimtar matsalar, sai kukunna sauti.
0

Ina da shekaru15 a lokacin da na tafi don in zauna da kawuna. A lokacin da na kai ‘yar shekara 16, sai kawuna ya umurce ni da in auri daya daga cikin ɗalibansa. Sai na ƙi, amma dai ya tursasa mini, aka kuma aurar da ni.

https://www.unfpa.org/ha/unheardvoices/farida
Danna ka saurara

Ina da shekaru15 a lokacin da na tafi don in zauna da kawuna. A lokacin da na kai ‘yar shekara 16, sai kawuna ya umurce ni da in auri daya daga cikin ɗalibansa. Sai na ƙi, amma dai ya tursasa mini, aka kuma aurar da ni.

Na kasa ci gaba da karatuna saboda mijina ya hana ni.

Mun bargari sakamakon harin da mayaƙan Boko Haram suka kai a ƙauyenmu. Tun lokacin da rayuwarmu ta kasance a sansanin ‘yan gudun hijira, sai mijina ya riƙa karbe duk wani tallafi da na samu, daga baya kuma ya tafiyarsa na tsawon makwanni. Na kasance da auren fuskantar bakin ciki na tsawon shekaru. Da ba tursasa mini in yi aure ba, da zan kasance cikin farin ciki a maimakon halin da na shiga.

story-letter
*An canza sunan domin matsalar tsaro

Tauye wa yara mata hakkin zaɓen wanda suke so su aura da lokacin da za su yi aure,nau’i ne na cin zarafi da ya shafi jinsi, wanda kuma ke  yaduwa sannu a hankali.

A TSAWATA. A DAINA CIN ZARAFIN JINSI
WANDA YA ƊAUKI HOTUNA SHI NE: Etinosa Yvonne