loading-texture
MURYOYIN DA BA A SAURARA BA
Waɗannan labarai na ɗauke ne da cikakkn bayani game da musgunawa da tashin hankali da cin zarafin da ya shafi sad
Domin kara fahimtar matsalar, sai kukunna sauti.
0

Babana ya aurar da ni ina ‘yar shekara 14. A lokacin ina makarantar firamare amma sai aka sa na dakatar da karatuna. Aurenmu ke da wuya sai duka ya fara. Sau biyu da dukan ya yi tsanani sosai har na shiga cikin wani hali.

https://www.unfpa.org/ha/unheardvoices/Uwani
Danna ka saurara

Babana ya aurar da ni ina ‘yar shekara 14. A lokacin ina makarantar firamare amma sai aka sa na dakatar da karatuna. Aurenmu ke da wuya sai duka ya fara. Sau biyu da dukan ya yi tsanani sosai har na shiga cikin wani hali.

Na yanke hukunci cewa ina so a sake ni, idan ya yarda zan ci gaba da rayuwa, idan ba haka ba, dole in jira.

Mijina ba ya kawo muna abubuwan buƙatun rayuwar yau-da-kullum a gida. Sau da dama dole nake tura ‘ya’yana domin su yi bara don na samu kuɗin da zan saya musu abinci. Ban taɓa jin daɗin rayuwar aure ba. Kwata-kwata ba na kallon kaina a matsayin matar aure.

story-letter
*An canza sunan domin matsalar tsaro

Mata da yawa na fuskantar rayuwa cikin yanayin rashin zaɓin makoma.

A TSAWATA. A DAINA CIN ZARAFIN JINSI
WANDA YA ƊAUKI HOTUNA SHI NE: Etinosa Yvonne