loading-texture
MURYOYIN DA BA A SAURARA BA
Waɗannan labarai na ɗauke ne da cikakkn bayani game da musgunawa da tashin hankali da cin zarafin da ya shafi sad
Domin kara fahimtar matsalar, sai kukunna sauti.
0

Muna shirin mu ranta cikin na kare kenan, sai aka kashe mijina. Ni kuma da ‘ya’yana aka kama mu. Aka tilasta mana tafiya kasa. Ya ɗauke mu tsawon kwanaki biyar kafin mu isa cikin jeji.

https://www.unfpa.org/ha/unheardvoices/Bakuwa
Danna ka saurara

Muna shirin mu ranta cikin na kare kenan, sai aka kashe mijina. Ni kuma da ‘ya’yana aka kama mu. Aka tilasta mana tafiya kasa. Ya ɗauke mu tsawon kwanaki biyar kafin mu isa cikin jeji.

Sai da muka yi tafiyar kwanaki 11 kafin sojoji su ceto mu.

Wato shekaru uku bayan rayuwata a jeji, na samu damar kuɓuta ni da ‘ya’yana. Tun lokacin da na samu ‘yancin kaina nike guje wa wuri mai hayaniya saboda irin wannan yanayi yakan firgita ni.

story-letter
*An canza sunan domin matsalar tsaro

Kowace mata ko yarinya da ta rayu bayan shiga halin tsananin uƙuba, to tilas ne ta samu taimako da kulawa game da kiwon lafiya na ƙwaƙwalwa. Idan sun kasa samun haka, to za su ci gaba da kasancewa ne cikin ukubar,halin da su kadai suka san abinda suke ciki.

A TSAWATA. A DAINA CIN ZARAFIN JINSI
WANDA YA ƊAUKI HOTUNA SHI NE: Etinosa Yvonne