loading-texture
MURYOYIN DA BA A SAURARA BA
Waɗannan labarai na ɗauke ne da cikakkn bayani game da musgunawa da tashin hankali da cin zarafin da ya shafi sad
Domin kara fahimtar matsalar, sai kukunna sauti.
0

Mahara sun kashe mijina na farko. Mun kuma yi hijira zuwa sansanin ‘yan gudun hijira. Al’amura sun yi tsauri matuƙa, bayan mutuwar mijina. Na kasa in iya ɗaukar nauyin kaina ballantana na‘ya’yana.

https://www.unfpa.org/ha/unheardvoices/jamila
Danna ka saurara

Mahara sun kashe mijina na farko. Mun kuma yi hijira zuwa sansanin ‘yan gudun hijira. Al’amura sun yi tsauri matuƙa, bayan mutuwar mijina. Na kasa in iya ɗaukar nauyin kaina ballantana na‘ya’yana.

Al’amura suka rincaɓe. Ɗana ya fara bara saboda mu samu abin da za mu ci.

A shekarar 2017 na samu ciki. Mijina bai kawo mini kowane nau’in gudummuwa ba. Da na tafi a kan cewa aure zai rage mini wahalhalun rayuwa, sai kuma abin ya kasance akasin haka.

story-letter
*An canza sunan domin matsalar tsaro

Duk da cewa labarin Jummai ya kasance na musamman ne a gareta, fuskantar cin zarafi daga abokin zama, abu ne da ya zama ruwan dare a wurare da dama a cikin duniya.

A TSAWATA. A DAINA CIN ZARAFIN JINSI
WANDA YA ƊAUKI HOTUNA SHI NE: Etinosa Yvonne