loading-texture
MURYOYIN DA BA A SAURARA BA
Waɗannan labarai na ɗauke ne da cikakkn bayani game da musgunawa da tashin hankali da cin zarafin da ya shafi sad
Domin kara fahimtar matsalar, sai kukunna sauti.
0

A lokacin da nike ‘yar shekara 12, wanda yake ɗan uba a gare ni, ya sanar da ni cewa yana son in auri wanda yake ɗan uba a gare shi. A wannan lokaci, shi ɗan uban nasa yana cikin shekarunsa na talatin da ‘yan kai.

https://www.unfpa.org/ha/unheardvoices/hamida
Danna ka saurara

A lokacin da nike ‘yar shekara 12, wanda yake ɗan uba a gare ni, ya sanar da ni cewa yana son in auri wanda yake ɗan uba a gare shi. A wannan lokaci, shi ɗan uban nasa yana cikin shekarunsa na talatin da ‘yan kai.

Watakila haka aka ƙaddara rayuwata ta kasance, ko kuma dai auren ne sanadin rusa rayuwar tawa.

Yayin da nake ƙoƙarin sake aure, sai mijina ya samu labarin baikona. Sai ya tuntuɓi iyayena ya sanar da su cewa bai sake ni ba. Iyayena suka aminta da maganarsa sannan suka ba ni umarnin in koma gare shi. Na gudu da ɗiyata zuwa. Dole na shiga harkar karuwanci. Iyayena suka ƙi ni. Mutane suna kiran ‘ya’yana shegu. Wani lokaci ina yi wa kaina addu’ar mutuwa saboda a ƙalla ‘ya’yana ba za su ci gaba da fuskantar tsangwama ba.

story-letter
*An canza sunan domin matsalar tsaro

Hafsat ba ta kasance matar farko ba — kuma ba ta zama ta ƙarshe ba —wadda salsalar rayuwarta ta kasance cikin tsananin ƙunci tun lokacin da aka yi mata auren dole.

A TSAWATA. A DAINA CIN ZARAFIN JINSI
WANDA YA ƊAUKI HOTUNA SHI NE: Etinosa Yvonne