loading-texture
MURYOYIN DA BA A SAURARA BA
Waɗannan labarai na ɗauke ne da cikakkn bayani game da musgunawa da tashin hankali da cin zarafin da ya shafi sad
Domin kara fahimtar matsalar, sai kukunna sauti.
0

An aurar da ni a lokacin da ni ke ‘yar shekara 12. Na ɗauki ciki a yayin da na cika shekara 14. Watanni kaɗan bayan na dauki ciki, sai aka sanar da ni cewa ina da cutar hawan jini tare da lamarin jijjigar jiki. Bayan da na haihu, an kwantar da ni a asibiti sakamakon ciwon. Na kasance ba ni gani ko iya magana. Na fara gani bayan kwanaki 25, bayan watanni 3 kuma sai na fara yin magana.

https://www.unfpa.org/ha/unheardvoices/halima
Danna ka saurara

An aurar da ni a lokacin da ni ke ‘yar shekara 12. Na ɗauki ciki a yayin da na cika shekara 14. Watanni kaɗan bayan na dauki ciki, sai aka sanar da ni cewa ina da cutar hawan jini tare da lamarin jijjigar jiki. Bayan da na haihu, an kwantar da ni a asibiti sakamakon ciwon. Na kasance ba ni gani ko iya magana. Na fara gani bayan kwanaki 25, bayan watanni 3 kuma sai na fara yin magana.

Na fahimci yana sone ya yi mini fyaɗe, saboda haka na roke shi, amma bai saurare ni ba.

Bayan watanni, sai muka bar tsakiyar gari muka kuma fara rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira. A ƙarshe na haifi ɗa, amma ya rasu bayan watanni biyar. A da, nikan yi kuka ainun; kuma nikan kasance cikin baƙin ciki saboda mutane kan tsangwame ni, a lokacin da nike da ciki. Yanzu ina ƙoƙarin in ci gaba da gudanar da rayuwata, na kuma bar komai a hannun Ubangiji.

story-letter
*An canza sunan domin matsalar tsaro

Mata a duk faɗin duniya, na cancantar samun gudunmuwa da tausayawa – ba zargi ko tsangwama ba game da halin ƙunci da suke jurewa.

A TSAWATA. A DAINA CIN ZARAFIN JINSI
WANDA YA ƊAUKI HOTUNA SHI NE: Etinosa Yvonne